Facebook Twitter
in Web www.nyscout.com
An turo kungiyoyin masu aikin jinya guda 7 zuwa Wuhan
2020-01-26 17:42:50        cri

Daraktan hukumar lafiya ta kasar Sin Ma Xiaowei ya bayyana a yayin taron manema labaru da aka shirya a yau Lahadin cewa, ya zuwa yanzu gwamnatin kasar Sin ta riga ta samar da kudin Sin RMB biliyan 1 don tallafawa lardin Hubei na kasar wajen rigakafi da shawo kan cutar numfashi ta coronavirus. Kana an riga an aike da kungiyoyin aikin jinya guda 7 dake shafar mutane sama da 900 zuwa lardin, kuma akwai wasu da suka gama share fage don zuwa lardin a duk lokacin da ake bukata. Baya ga haka, rundunar soji ta kuma aike da kungiyar masu aikin jinya dake kunshe da ma'aikatan lafiya 450, a waje guda kuma kungiyoyin guda 8 masu kunshe da mutane sama da 1000 a shirye suke don tashi zuwa birnin na Wuhan. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China

 

湖北11选5走势图